Shugaba Tinubu ya nemi Malaman Addini su koma Nijar karo na biyu
Shugaba Tinubu ya nemi Malaman Najeriya su koma Nijar karo na biyu Shugaba Bola Tinubu ya umarci ayarin malaman addinin Musulunci da ke shiga tsakani a rikicin Jamhuriyar Nijar su koma wajen shugabannin mulkin sojin ƙasar don samo wani ƙwaƙƙwaran alƙawari. Bayan wani taron sirri da malaman, jagoran tafiyar, Ustaz Abdullahi Bala-Lau ya ce Tinubu na neman a kauce wa amfani da ƙarfi don warware rikicin, kuma a tabbatar an mayar da Nijar kan tafarkin tsarin mulki. Ya ce Tinubu ya karɓi shawarwarinsu na a kauce wa amfani da ƙarfin soja wajen kawo ƙarshen duk wata taƙaddama, musamman ma a tsakanin maƙwabta da manyan ƙawaye na tsawon lokaci. A ranar Laraba ne, malaman addinin Musuluncin suka koma Nijar a karo na biyu, inda suka gana Shugaba Abdurahamane Tchiani da Firaminista Ali Lamine Zeine, kafin su dawo Abuja don yi wa Shugaba Tinubu bayani a kan matsayar da suka cimma. Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito Sheikh Bala-Lau ya ce: "Wannan ce ta sa ya sake c...